Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-21 17:35:50    
Watakila tattalin arzikin duniya zai iya fitowa daga mawuyacin hali a shekara mai zuwa

cri
A ran 21 ga wata, Murilo Portugal, mataimakin shugaban asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya yi bayani a birnin Beijing, cewar idan kasashe daban daban za su iya samun kyawawan sakamako wajen tinkarar matsalar kudi, to watakila tattalin arzikin duniya zai iya fitowa daga mawuyacin hali sannu a hankali a shekara mai zuwa. A waje daya kuma ya kiyasta cewa, karuwar tattalin arzikin duniya za ta ragu da kashi 0.5 zuwa kashi 1.5 cikin kashi dari a shekarar bana.

Lokacin da yake halartar taron koli na kara wa juna ilmi na taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa tsakanin manyan matakai kan bunkasuwar kasar Sin na shekara ta 2009, Mr. Portugal ya bayyana cewa, wani muhimmin karfi wajen farfado da tattalin arzikin duniya shi ne yin kwaskwarima kan hukumomin kudi. Idan kasashe daban daban za su iya samun kyawawan sakamako a lokacin zafi ko bayan watan Yuni na shekarar da muke ciki a cikin ayyukan yin kwaskwarima kan hukumomin kudi, to watakila tattalin arzikin duniya zai iya samun farfadowa a shekara mai zuwa.(Kande Gao)