Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 17:03:25    
Kada a manta da kasashe mafi talauci yayin da ake fama da matsalar kudi

cri

A ran 13 ga wata a nan Beijing, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, kada a manta da kasashe mafi talauci yayin da ake fama da matsalar kudi da ba a taba gani ba. A gun taron koli na kungiyar kasashen 20, ya kamata a mai da hankali kan taimakawa kasashe masu ci gaba musamman ma kasashe mafi talauci. Mista Wen Jiabao ya yi wannan bayani yayin da yeke amsa tambayar manemi labaru na kasar Afrika ta kudu a gun taron ganawa da manema labaru bayan da aka rufe taron majalisar wakilan jama'ar Sin.

Mista Wen Jiabao ya ce, kada a canja burin raya kasa da kasa na M.D.D. a cikin sabon karni. Kasar Sin kasa ce mai ci gaba da ta fi girma a duniya. Kafin shekarar 2008, Sin ta soke basusuka na kasashe 46 da suka mafi talauci, yawansa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 40. A shekarar da ta gabata, kasar Sin ta yi alkawarin ci gaba da soke duk sauran basusukan kasashe mafi talauci har zuwa karshen shekarar 2008. Ban da wannan kuma, Sin ta soke haraji na kashi 95 cikin dari daga cikin kayayyakin da wadannan kasashe suka fitar zuwa Sin.

Bugu da kari, Wen Jiabao ya ce, kasar Sin za ta ba da karin tallafi ga Afrika wajen gina makarantu da asibitoci, da kara yawan daliban Sin da za su yi karatu a Afrika, kana da aikawa da karin mutanen da suke ba da jiyya da ba da ilmi zuwa wadannan kasashe don taimakawa musu.(Asabe)