Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 17:02:11    
Wen Jiabao ya bukaci kasar Sin da ta tabbatar da ingancin kudin Sin

cri
A ran 13 ga wata, firayim ministan Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, kasar Sin kasa ce ta ba da basussuka mafi yawa ga Amirka, shi ya sa ta mai da hankali sosai kan ingancinsu. Ya jaddada cewa, bangaren Sin yana bukatar Amirka da ta cika alkawarinta na tabbatar da ingancin kudin Sin.

A ran nan, an rufe taron majalisar wakilan jama'ar Sin. Yayin da yake amsa tambayar manema labaru a gun taron manema labaru da aka yi bayan taron, mista Wen Jiabao ya ce, kasar Sin tana a matsayin kasar da ta ba da basussuka mafi yawa ga Amirka, kuma Amirka ta fi bunkasuwa a fannin tattalin arziki a duniya, sabo da haka, Sin tana mai da hankali sosai kan bunkasuwar tattalin arzikin Amirka, da fatan ganin yadda sabuwar gwamnatin Amirka ta shugaba Barack Obama ta dauki matakan tinkarar matsalar kudi.

Ban da wannan kuma, Wen Jiabao ya nanata cewa, bayan gyare-gyare da ayyukan raya kasa da aka yi a cikin shekaru da suka gabata, kasar Sin ta ajiye kudaden musaya da yawa, wanda ya nuna karfin tattalin arzikinta. Ya ce, a kan wannan lamari, Sin za ta kare moriyar kasa da farko, a sa'I daya kuma yin la'akari da dukkan kasuwannin kudi na kasa da kasa.(Asabe)