A ran 13 ga wata, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana a birnin Beijing cewa, samun karuwar GDP da kashi 8% da aka bayar a shekarar bana alkawari ne da gwamnatin Sin ta yi bayan da ta yi la'akari da bukatu, wanda ya bayyana imanin gwamnatin Sin da fatanta.
A wannan rana, an rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. Bayan da aka rufe taron, firayin ministan Sin Wen Jiabao ya bayyana wannan a taron maneman labaru. Game da samun karuwar GDP da kashi 8% da ya jawo hankalin kasa da kasa, Wen Jiabao ya ce, ko da yake yana da wuya wajen cimma wannan buri, amma mai yiwuwa ne za a cimma burin idan aka yi namijin kokari.
Wen Jiabao ya ce, a cikin rahoton aikin gwamnati da aka bayar a ran 5 ga wata, an ba da bayanai game da yiwuwar cimma burin karuwar GDP da kashi 8%.(Zainab)
|