Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 16:35:23    
Wen Jiabao ya nuna cewar kasar Sin ta share fagen warware matsalar kudi ta duniya a cikin dogon lokaci

cri

A ran 13 ga wata, a birnin Beijing, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya nuna cewa, kasar Sin ta share fagen warware matsalar kudi ta duniya a cikin dogon lokaci, kuma Sin za ta iya gabatar da manufofi a wane lokaci don sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki.

Wen Jiabao ya furta haka ne a lokacin da ya yi wata ganawa da manema labaru, inda ya furta cewa, gwamnatin kasar Sin ta shriya manufofin don warware matsalar kudi, wato ta shirya wani daftari don warware matsalar dake da tsanani.

Ya nuna cewa, gwamnatin Sin ta gabatar da kudurin yin amfani da kudin Sin Yuan biliyan 4000 don sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki, kuma bayan kokarin da aka yi a cikin watanni 6 da suka wuce, ya zama kuduri sosai.

Wen Jiabao ya nuna cewa, zuba jarin gwamnati shi ne mataki mafi karfi na sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki. A cikin jarin da gwamnatin Sin ta zuba, da akwai ayyukan da aka shirya, dole ne a sa kaimi ga batun bunkasuwar wadannan ayyukan, za a yi amfani da kudin Sin yuan biliyan 1180 da gwamnatin ta zuba don habaka ayyukan rayuwar jama'ar Sin. (Abubakar)