Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 10:12:29    
An rufe taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na shekarar bana

cri
A ranar 13 ga watan Maris da safe, an rufe taro na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11 a nan birnin Beijing, inda aka samu halartar shugabannin kasar Sin kamarsu Hu Jintao,da Wu Bangguo, da Wen Jiabao, da Jia Qinlin, da dai sauransu.

A wajen taron an zartas da kudurori game da rahoto kan aikin gwamnati, da yadda aka tafiyar da shirin raya tattalin arziki da al'umma a shekarar 2008, da sabon shirin na shekarar 2009, da yadda aka yi amfani da kasafin kudi a shekarar 2008, da shirin kasafin kudi na shekarar 2009, da kuma rahoto kan aikin kotun kolin kasar.Sa'an nan an nuna amincewa kan rahoton aikin gwamnatin kasar, da shirin raya tattalin arzki da al'umma na shekarar 2009, da kasafin kudi na shekarar 2009, da rahotannin da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ,da kutun koli, da kuma hukumar bin bahasi da gabatar da kara suka bayar.

Sa'an nan a wajen bikin rufe taron, Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya ba da jawabi.(Bello Wang)