Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 17:42:41    
Masana'antu masu zaman kansu na Sin sun ba da gudummawa sosai wajen bunkasa harkokin jin dadin jama'a na Afrika

cri

A ranar 11 ga wata, a nan birnin Beijing, yayin da mataimakiyar sakatare janar ta kwamitin kula da harkokin cinikayya ta jama'ar Sin da Afrika Madam Zhang Li ke zantawa da manema labaru, ta bayyana cewa, ba ma kawai masana'antu masu zaman kansu na Sin da suka zuba jari a Afrika sun cusa sabbabin abubuwa wajen bunkasa tattalin arziki na wurin ba, haka kuma sun ba da gudummawa sosai wajen bunkasa harkokin jin dadin jama'a na Afrika.

Madam Zhang Li ta bayyana cewa, babban nauyin da ke bisa wuyansu, shi ne jagoranta da taimakawa masana'antu masu zaman kansu masu karfi na Sin da suka shiga kasuwannin Afrika. Yayin da wadannan masana'antu suka samu moriya a fuskar tattalin arziki, kana kuma sun ba da gudummawa sosai wajen bunkasa harkokin jin dadin jama'a na Afrika. Ya zuwa yanzu, masana'antu masu zaman kansu na Sin da suka zuba jari a Afrika suna gudanar da ayyukan gina makarantu da asibitoci da kafa asusun raya sha'anin ilmi da dai sauransu. Zhang Li ta bayyana cewa, sauke nauyin da ke bisa wuyansu zai taimaka wa masana'antu masu zaman kansu na Sin da su ci gaba da kafawa da bunkasa siga mai kyau ga Afrika. (Bako)