Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 20:24:14    
Manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje babban makami ne ga Sin wajen tinkarar matsalar kudi ta duniya

cri

A ran 10 ga wata, firaministan kasar Sin, Mr.Wen Jiabao ya bayyana cewa, manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje wani muhimmin zabi ne da ya tabbatar da makomar kasar Sin, haka kuma wani babban makami ne ga kasar wajen tinkarar matsalar kudi da ke galabaitar da kasashen duniya. Ya ce, a mawuyacin halin da ake ciki, kamata ya yi a tsaya ga bin manufar ba tare da kasala ba.

A ran nan, Mr.Wen Jiabao ya halarci shawarwarin tawagar wakilan jihar Mongoliya ta gida a gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, inda ya ce, tilas ne a aiwatar da manufar yin gyare-gyare da kirkire-kirkire zuwa fannoni daban daban da ke shafar mulkin kasa, a yi ta kyautata hanyar ci gaba da ke da sigar musamman ta Sin, don samar da kuzari da kuma tabbaci ga ci gaban kasa. Sa'an nan, tilas ne a tsaya ga bin manufar bude kofa ga kasashen waje, ta yadda za a sami sabon fifiko wajen hadin gwiwa da kasashen waje ta fannin tattalin arziki.(Lubabatu)