Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 16:50:20    
Aikin samar da damar samun aiki na kasar Sin ya samu kyautatuwa

cri

A ran 10 ga wata, Yin Weimin, ministan kula da harkokin kwadago da ba da tabbacin zaman al'umma na kasar Sin ya bayyana cewa, aikin samar da damar samun aiki na kasar Sin ya samu kyautatuwa. A watan Janairu na bana da watan Fabrairu, yawan sabbin gurabun aiki na birane da na garuruwa ya fara karuwa.

A gun taron manema labaru na taron majalisar wakilan jama'ar Sin a mataki na biyu a karo na 11, Yin Weimin ya ce, a karkashin manufofin da abin ya shafa, a wadannan matanni biyu, yawan sabbin kwadago na birane da na garuruwa na kasar Sin ya kai dubu 690 da dubu 930, wannan ya karu sosai bisa na watan Nuwamba na shekarar bara da na watan Disamba.

Bugu da kari, Yin Weimin ya ce, sakamakon matsalar kudi da ake fama da ita, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ta sassauta, yawan sabbin gurabun aiki na birane da na garuruwa ya ragu sosai, aikin samar da damar samun aiki ya fi tsamari.(Asabe)