Bisa sakamakon da hukumar yin kiddidiga ta kasar Sin ta bayar a ran 10 ga wata, an ce, a watan Febrairu na shekarar bana, yawan ma'aunin farashin kayayyakin da jama'a ke amfani da su wato CPI na kasar Sin ya ragu da kashi 1.6% bisa na makamancin lokacin bara, wanda ya zama lokaci na farko ne da farashin kayayyakin Sin ya ragu a cikin shekaru 6 da suka wuce.
Farashin abinci ya ragu da kashi 2%, kuma farashin kayayyakin da jama'a suke saya ya ragu da kashi 1.5%. Adadin CPI na kasar Sin ya yi daidai da na watan Janairu na shekarar bana.
A shekarar 2008, yawan CPI na kasar Sin ya karu da kashi 5.9% bisa na makamancin lokacin shekarar 2007. A ran 5 ga wata, yayin da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao yake gabatar da rahoton aikin gwamnati a taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya bayyana cewa, kamata ya yi karuwar CPI na shekarar bana ta kai kashi 4%.(Zainab)
|