Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-09 15:12:41    
Kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin yana yin kokari wajen sa kaimi wajen kafa dokokin ta hanyar kimiyya da dimokuradiyya

cri
A cikin wani rahoto a kan ayyukan kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da shugaban kwamitin Wu Bangguo ya gabatarwa wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ran 9 ga wata, ya ce, a cikin ayyukan kafa dokokin da aka yi bara, kwamitin yana yin kokari wajen sa kaimi wajen kafa dokokin ta hanyar kimiyya da dimokuradiyya.

Wu Bangguo ya nuna cewa, bisa kudurin da taron kwamitin din-din-din na mambobi na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya tsai da, za a sanar da duk daftarorin da kwamitin ya duba ta kafar internet na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma za a sanar da muhimman daftarorin ta kafofin watsa labaru na kasar Sin, da neman ra'ayoyi daban daban da tafiyar da aikin kafa dokoki yadda ya kamata. A sa'i daya, hukumomin kafa dokokin za su yi biciken muhimman batutuwan da ke a cikin daftarorin, kuma za a yi shawarwari tare da bangarorin da abin ya shafa ta hanyar musayar ra'ayoyi da taron tattaunawa, don samun hanyoyin warware batutuwan, da kuma kyautata wadannan daftarorin.(Abubakar)