|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-03-09 14:15:11
|
Kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya mai da hankali kan batun ingancin abinci
cri
A cikin wani rahoto a kan ayyukan kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da shugaban kwamitin din Wu Bangguo ya gabatarwa wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ran 9 ga wata, an ce, ingancin abinci nada alaka da lafiyar jama'a da rayuwarsu, sabo da haka, wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da jama'a na fannoni daban dan sun mai da hankali a kan batun ingancin abinci.
Lokacin da aka kafa dokar kiyaye ingancin abinci, an samu batun gurbataccen garin madara na kamfanin Sanlu. Game da wadannan batutuwan rashin ingancin abinci, kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya kara gyaran shirin dokar ingancin abinci bayan ya yi bincike kuma ya samu ra'ayoyin daban daban.(Abubakar)
|
|
|