Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-11 21:52:12    
Wu Bangguo ya gana da firaministan kasar Habasha Meles Zenawi

cri

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo wanda ke yin ziyara a kasar Habasha ya gana da firaministan kasar Habasha a ran 10 ga wata a birnin Addis Ababa.

Wu Bangguo ya furta cewa, kasar Sin ta mai da kasar Habasha a matsayin abokiyar hadin gwiwa da za ta iya amincewa da ita, tana son ta zurfafa zumuntan dake tsakaninsu da kara hadin gwiwa tare da kasar Habasha don ingiza bunkasuwar huldar abokantaka ta hadin gwiwa a dukkan fannoni a tsakaninsu. Ya shawarci shugabannin kasashen biyu da su rika tuntubar juna da kara musanyar ra'ayi da hadin gwiwa tsakanin jam'iyyu da hukumomin tsara dokoki da gwamnatoci na kasashen biyu. Sa'anan, yana fatan za su kara hadin gwiwa don gudanar da aikin cibiyar nuna fasahohin noma da sauran ayyuka 7 da taron koli na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Afrika ya tsara da kyau. haka kuma ya ba da shawara cewa, ya kamata a aiwatar da jerin ayyukan hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da ciniki, cik har da tashar samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da karfin ruwa da kuma kafa unguwar masana'antu mai inganci. Bangaren Sin ya kalubalanci kamfannonin kasar Sin da su kara zuba jari a kasar Habasha, da bayar da manufofi masu gatanci ga aikin sayar da fasahohi, da kuma kara kula da ayyukansu a kasar Habasha da horar da masana ayyukan fasaha don samar da karin ayyukan yi. Ya kuma kara da cewa, ya kamata kasashen biyu su kara musanyar ra'ayi da cimma daidaito kan harkokin duniya don kiyaye moriyar kasashen biyu da ta dukkan kasashe masu tasowa bisa doka.(Lami)