Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-11 13:14:48    
Sin na daukar kwararan matakai domin tinkarar matsalar hada-hadar kudi

cri
Firaminista Wen Jiabao na kasar Sin ya bayyana ranar 10 ga wata cewar, halin da ake ciki a gida da waje na kara kamari, shi ya sa abin da ya kamata gwamnatin Sin ta ba fifiko shi ne tabbatar da raya tattalin arziki gadan-gadan kuma cikin sauri, da yin riga-kafin matsalar tangal-tangal fiye da kima a kasuwannin kudade.

Jiya a nan birnin Beijing, majalisar gudanarwa ta Sin ta kira taron manyan jami'ai na gwamnatocin larduna da na birane da na sassan majalisar gudanarwa ta kasar Sin, inda firaminista Wen Jiabao ya yi jawabi cewar, domin kawar da mummunar illar da matsalar hada-hadar kudi da ta zama ruwan dare a duniya ta kawowa habakar tattalin arzikin Sin, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwa ta kasar sun yanke shawara kwanan baya cewa, ya kamata a aiwatar da manufar tattalin arziki cikin himma da kwazo da manufar kudi kamar yadda ya kamata, da tsaurara matakan daukaka cigaban tattalin arzikin Sin.

A waje daya kuma, babban bankin kasar Sin, wato bankin jama'ar kasar Sin ya bayyana jiya cewar, zai tsara hakikanan matakai, domin bada hidimomin kudi daban-daban, ciki har da kara biyan bukatun jama'a cikin gida, da tabbatar da bunkasar tattalin arziki cikin sauri. Matakan da bankin jama'ar kasar Sin zai dauka sun hada da, na farko, a bada tabbaci ga musayar isassun kudade a kasuwannin kudi. Na biyu, a tabbatar da karuwar rancen kudin da ake bayarwa. Na uku, a bada kwarin-gwiwa da jagoranci sassan kudi da su kara samar da tallafin kudi ga kanana da matsakaitan kamfanoni, da aikin gona, da ayyukan sake farfadowa bayan aukuwar mummunan bala'i.(Murtala)