Bayan gwamnatin kasar Sin ta fitar da matakai guda 10 a ran 9 ga wata don ci gaba da kara biyan bukatun cikin gida da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki lami lafiya, wasu shugabannin kasashen waje da kafofin watsa labaru sun mai da hankulansu a kan wadannan matakai kuma sun nuna yabo bi da bi.
A ran 10 ga wata, firayin ministan kasar Australia Mr.Kevin Rudd ya nuna cewa, matakai guda 10 masu sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki suna da muhimmiyar ma'ana, sun bayyana gwamnatin kasar Sin ta mai da hankalinta a kan bunkasuwarta a cikin gida. Kuma a ganninsa, wandannan matakai kyakyawan albishir ne ga tattalin arziki na kasar Australia da sauran yankuna na duniya.
Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta bayar da labarin cewa, a gannin masanan ilmin fannin tattalin arziki, wandannan matakai za su sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin da ya karu da kashi biyu bisa dari a shekarar mai zuwa. Bankin Morgan Stanley na kasar Amurka ya bayyana cewa, wadannan matakai sun shaida cewa, gwamnatin kasar Sin tana son kara imani na kamfanonin masu zaman kansa ta hanyar yin alkawarin tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri.(Abubakar)
|