Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-11 10:08:53    
Shugaban zaunannen kwamitin wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya isa kasar Madagascar

cri
Bisa gayyatar shugaban majalisar dokoki ta kasar Madagascar Jacques Sylla da ta shugaban majalisar dattijai ta kasar Yvan Randriasandratriniony, shugaban zaunannen kwamitin wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya isa Tananarive a ran 10 ga wata da dare bisa agogon wurin, don fara ziyarar aiki ta sada zumunci a kasar Madagascar.

A cikin ziyararsa, Mr. Wu Bangguo zai gana da yin shawarwari tare da shugaban kasar Madagascar, firayim ministan kasar, shugaban majalisar dokoki ta kasar, shugaban majalisar dattijai ta kasar da sauran shugabannin kasar, inda za su musaya ra'ayoyinsu a kan dangantaka tsakanin bangarori biyu da batutuwan dake jawo hankalin kasashen biyu.

Kasar Madagascar ita ce zango na hudu da Mr. Wu Bangguo ya kai ziyara a kasashen Afrika biyar, kafin Madagascar ya kai ziyararsa a kasashen Algeria, Gabon, Habasha bi da bi, kuma zai kai ziyararsa a kasar Seychelles.(Asabe)