Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 21:26:26    
Mutanen da yawansu ya kai 69226 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan

cri
Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da sanarwa a ranar 8 ga wata cewa, ya zuwa ranar 8 ga watam Satumba da karfe 12, mutanen da yawansu ya kai 69226 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da mutane 374643 suka ji rauni, kuma mutane 17923 suka bace.

Bayan haka kuma, bisa rahoton da ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar an ce, ya zuwa ranar 8 ga wata da karfe 12, kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyaki masu darajar kudin Sin RMB biliyan 59.3 daga bangarori daban daban na gida da waje.

Har wa yau kuma, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta bayar da rahoto cewa, ya zuwa ranar 8 ga wata da karfe 12, gwamnatoci na matakai daban daban na kasar Sin sun bayar da kudin Sin RMB biliyan 67.4 kan ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da na ceto. (Bilkisu)