Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-05 15:20:25    
An kammala aikin mika wutar wasannin Olympic na nakasassu na yau a nan birnin Beijing

cri

Yau da safe da misalin karfe 10 da mintoci 20, aka kammala aikin mika wutar wasannin Olympic na nakasassu a nan birnin Beijing. Gobe, za a mika wutar a lambun sha iska na Chaoyang.

Tsawon hanyar da aka bi wajen mika wutar na yau ya kai kilomita 6.4, da akwai masu mika wutar 120, a cikinsu da akwai nakasassu 30. Da misalin karfe 8 da rabi na safe, wutar ta iso ginin cibiyar sabon karni ta kasar Sin, a sa'i daya kuma an kunna wutar dake cikin tukunya, daga baya, sai an kunna wuta ta farko da za a mika a nan birnin Beijing. In an kammala mika wutar a lambun shan iska na Chaoyang gobe da safe, za a kai wutar zuwa filin wasannin motsa jiki na kasar Sin don kunna babbar wuta a lokacin da za a yi bikin bude wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a ran nan.(Asabe)