Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 19:19:20    
An tabbatar da mai rike tuta ta kungiyar wakilan 'yan wasannin Olympics ta kasar Nijeriya

cri

A ranar 8 ga wata a nan birnin Beijing, wani jami'in kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Nijeriya ya sanar da cewa, 'yar wasan kwallon tebur ta kasar Bose Kaffo za ta zama mai rike tuta ta kungiyar wakilan kasar a gun bikin bude wasannin Olympics na Beijing.

Kaffo ita ce tsohuwar 'yar wasan kwallon tebur ta Afrika, wannan ne karo na biyar da ta shiga wannan gaggarumin bikin wasannin motsa jiki, tun bayan da ta halarci wasannin Olympics na Barcelona a shekarar 1992.

Kungiyar wakilan kasar Nijeriya ta kunshi mutane 153, ciki har da 'yan wasa 90, da jami'an kula da harkokin motsa jiki, da masu horar da 'yan wasa da yawansu ya kai 63. 'Yan wasannin kasar Nijeriya za su shiga wasannin kwallon kafa, da na guje guje da tsalle tsalle, da na kwallon tebur, da na kwallon badminton, da kuma wasan kokawa, da dai sauransu, kuma ana kyautata zaton cewa, za su samu lambobin yabo a wasannin guje guje da tsalle tsalle, da na kwallon kafa, da na daukan nauyi, da kuma na tackwando. (Bilkisu)