|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2008-08-08 17:57:01
|
An tabbatar da mai rike tuta na kungiyar wakilan kasar Niger a gun bikin bude wasannin Olympics
cri
A ranar 8 ga wata, kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Nijer, wadda ke halartar wasannin Olympics na Beijing, ta tabbatar da mai rike tutar kasarta a gun bikin bude wasannin Olympics.
Wani jami'in kungiyar wakilan kasar Niger ya fayyace cewa, 'dan wasan iyo na kasar Al-Housseini Lamine zai zama mai rike tutar kasar Niger na kungiyar wakilan kasar, da kuma shugabancin kungiyarsu don shiga filin wasanni.
Kungiyar wakilan kasar Niger ta kunshi mutane sama da 30, ciki har da 'yan wasa biyar, wadanda za su shiga wasannin guje guje da tsalle tsalle, da na iyo, da kuma na karate. (Bilkisu)
|
|
|