Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 13:45:23    
'Yar wasan gudun tsawon mita 800 ta Kenya ta share fage sosai wajen samun lambar zinari a gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri
A ran 7 ga wata, a birnin Beijing, Pamela Jelimo, 'yar wasan gudun tsawon mita 800 ta bayyana cewa, ta riga ta shirya, kuma za ta yi kokari kan samun lambar zinari ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ga kasar Kenya.

Lokacin da Jelimo ta zanka da 'yar jaridarmu, inda ta bayyana cewa, ta riga ta shirya sosai, kuma tana fatan za ta sami sakamako mai kyau, kuma za ta yi namijin kokari kan samun lambar zinari ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ga kasar Kenya. Jelimo ta ce, ko da yake yanayin Beijing da na Nairobi suna da bambanci, amma ta riga ta saba da yanayin Beijing, kuma yanayin ba zai kawo wa gasar tasiri ba.

Pamela Jelimo mai shekaru 18 a shekarar bana za ta zama 'yar takarar wasa da ke da babbar karfi wajen samun lambar zinari na wasan gudu na tsawon mita 800 a cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Zainab)