Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ranar sayayya ta Sin na iya karya matsayin bajimta a cewar kafar BBC
2020-11-11 10:45:57        cri

Kafar watsa labarai ta BBC, ta ce sakamakon ci gaba da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, akwai hasashen cewa miliyoyin jama'a za su yi sayayya a yau 11 ga watan 11, wadda ita ce ranar sayayya mafi girma ta kasar Sin.

Ranar sayayya ta kasar Sin, wadda ta yi kama da ranar "Black Friday" da ke gudana a yammacin duniya, rana ce da masu sayar da hajoji ke samar da garabasa ga masu sayayya, ita ce kuma rana daya tilo da a cikin sa'o'i 24 ake gudanar da sayayyar hajoji mafi yawa a duniya baki daya.

A makamanciyar wannan rana ta shekarar da ta gabata, masu sayayya sun yi odar kayayyaki da yawan su ya kai biliyan 1.9. Kaza lika a baran, cikin minti daya da 'yan dakikoki da shiga ranar 11 ga watan 11, an yi cinikin da ya haura na dalar Amurka Biliyan 1. Kafar BBC ta ce mai yiwuwa matakan kullen COVID-19, su sanya adadin sayayyar na yau ya zarta wadanda suka gabata a shekarun baya.

A bara, yayin hada hadar ranar cinikayyar ta ranar ta 11 ga watan 11, kamfanin sayayya ta yanar gizo na Alibaba wato TMall, ya yi cinikin kudin Sin sama da yuan biliyan 210, daidai da kusan dalar Amurka biliyan 31.7, adadin da ya haura jimillar cinikin da aka yi a ranekun "Black Friday" da "Cyber Monday" baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China