Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wane tasiri baje kolin CIIE zai yiwa tattalin arzikin duniya a lokacin annoba?
2020-11-09 17:18:51        cri

Yayin da duniya ta wari gari da barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 tun a farkon wannan shekara, al'amurran tattalin arzikin duniya, da yanayin zaman rayuwar al'umma, da walwalar al'umma ya shiga halin ha'ula'i samakon annobar duba da irin mummunan tasirinta ga dukkan fannonin rayuwar bil adama. Sai dai da alama, za mu iya cewa "kaya ne ya tsinke a gindin kaba", in ji 'yan magana, a wani kaulin, "abin nema ya samu, wai matakar makadi ta haifi ganga". A yanzu haka ana cigaba da gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin kasar Sin wato a takaice CIIE, a karo na 3, a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin. Za mu iya cewa bikin ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa, duba da irin halin da tattalin arzikin duniya ke ci gaba da fuskanta na durkushewa. Ko shakka babu, bikin baje lolin ya ja hankalin kasa da kasa duba da irin tasirinsa wajen tada komadar tattalin arzikin kasa da kasa a wannan matsanancin halin da aka shiga, domin zai haifar da da mai ido ga wannan hali da duniya ta tsinci kai cikinsa. Wannan dalili ya sa masa da dama suke cigaba da yin tsokaci gami da fashin baki dangane da bikin bajekolin na CIIE na wannan karo. Kamar yadda wani masanin kasar Morocco ya bayyana cewa jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a lokacin bude taron bikin na CIIE ya isar da wani muhimmin sako mai armashi ga duk duniya baki daya. A cewar masanin, kalaman shugaba Xi ya jawo hankalin masanan ketare matuka. Shugaban kungiyar hadin kai da samun bunkasuwar Afrika da Sin na kasar Morocco Nasser Bouchiba ya bayyana cewa, jawabin shugaba Xi ya bayyana aniyar kasar Sin na kara bude kofarta ga ketare, matakin da ba ma kawai ya samarwa duniya damammaki masu kyau ba ne, har ma ya goyi bayan kasashe masu tasowa.

Hakika wannan muhimminyar dama da kasar Sin ta samar na bude kofarta ga ketare zai kara ba da babbar gudunmawa wajen kyautata makomar tattalin arzikin duniya a wannan mawuyacin hali musamman kasashe masu tasowa. Duba da irin girma da kasuwannin Sin ke da shi musamman ta fuskar bukatun kayayyakin da ake shigo da su kasar, baje kolin CIIE zai taimaka gaya wajen bada dama ga kasashen duniya masu yawa dake kawance da kasar ta Sin wajen tada komadar tattalin arzikinsu daga babbar illar da annobar COVID-19 ta haifar musu. Da fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China