Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin kasar Sin ta shirya liyafar murnar ranar kafuwar kasa
2020-09-30 20:21:55        cri
Da yammacin yau ne, majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya wata liyafa a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, don murnar cika shekaru 71 da kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da firaminista Li Keqiang da sauran shugabannin kasar game da manyan baki Sinawa da na ketare kimanin 500 ne suka halarci bikin.

A jawabinsa firaminista Li Keqiang, ya ce, wannan shekarar ta sha bamban a tarihin Jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Ya ce, sakamakon barkewar annobar Covid-19, da mummunan tasirin karayar tattalin arzikin duniya, ya sa kasar ta dauki matakai a jere, don inganta matakan kandagarki da hana yaduwar annobar, da raya tattalin arziki da inganta rayuwar jama'a, baya ga kyakkyawan sakamakon da kasar Sin ta cimma wajen yaki da wannan annoba

Ya ce, tattalin arzikin kasar ya farfado, kana an kare rayukan jama'a yadda ya kamata. A don haka, ya kamata kasar ta karfafa imaninta, ta kuma tunkari duk wani kalubable da ka iya kunno kai tare da mayar da hankali kan abubuwan da ta sanya a gaba. Ya ce kamata ya yi kasar Sin ta kara zurfafa gyare-gyare da kara bude kofarta ga ketare. Haka kuma ya kamata daukacin al'ummar kasar baki daya, su kara zage damtse don cimma nasarar manyan manufofin da aka sanya gaba da ma burin da kasar ke fatan cimmawa a shekarar baki daya, da gina al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China