Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta ba da fifiko wajen samarwa kasashe masu tasowa alluran riga kafin COVID-19 ta hanyoyi daban-daban
2020-09-30 19:53:30        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, Kasarsa tana kokarin ganin ta samar da alluran riga kafin COVID-19, a kokarin da duniya ke yi na ganin bayan annobar.

Wang Wenbin ya bayyana haka ne Larabar nan, yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa. Yana mai cewa, bayan an kammala gudanar da binciken samar da rigakafin, da ma fara amfani da ita, kasar Sin ta yi alkawarin fara samar da riga kafin ne ga kasashe masu tasowa ta hanyoyi daban-daban, ciki har da ba da gudummawa da kuma taimakawa kyauta.

A baya-bayan nan ne, wasu kafofin watsa labarai suka ba da rahoton cewa, farashin alluran rigakafin a kasar Sin ya fi na Turai da Amurka tsada sosai. A kan wannan batu, Wang Wenbin, ya ce babu kamshin gaskiya kan wannan magana.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China