Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kasance kan gaba a duniya a kasuwar intanet cikin shekaru 7 a jere
2020-09-30 10:51:14        cri
Cibiyar tattara bayanai game da harkokin intanet ta kasar Sin, ta fitar da kididdiga karo na 46, game da ci gaban kasar a fannin intanet, jiya Talata, a birnin Beijing.

A cewar rahoton, Sin na da musu amfani da intanet miliyan 940 ya zuwa Yunin 2020, inda yawan amfani da intanet din ya kai kaso 67.0 cikin dari. Kana adadin masu amfani da intanet ta wayar salula ya kai miliyan 932, wanda ya mamaye kaso 99.2 na daukacin adadin masu amfani da kafar.

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, kasar Sin ita ce kasa mafi girman kasuwar intanet cikin shekaru 7 a jere, wato tun daga shekarar 2013 zuwa yanzu. Ya zuwa watan Yunin 2020, adadin masu amfani da intanet wajen sayayya a kasar Sin, ya kai miliyan 749, wanda ya dauki kaso 79.9 na jimilar masu amfani da intanet din.

Baya ga haka, kasuwar biyan kudi ta kafar intanet ta kasar Sin, ita ce ke kan gaba a duniya cikin shekaru 3 a jere. A farkon rabin shekarar 2020, adadin kudin da aka biya ta intanet a kasar Sin ya kai Yuan triliyan 196.98, wanda ya karu da kaso 18.61 a kan na bara, wanda kuma ke kan matsayi na 1 a duniya.

Bugu da kari, a rabin farkon bana, harkar cinikayya kai tsaye ta intanet, wanda ke zaman sabon nau'in kasuwanci, ya zama jigon bunkasa tattalin arziki irin na zamani.

Rahoton ya bayyana cewa, adadi mai yawa na dandalin cinikayya ta intanet da na wallafa gajerun bidiyo da na bincike da sauran dandalin intanet, sun gaggauta tsara ayyukan cinikayya kai tsaye ta intanet, kuma sun kunshi kyawawan dabaru da dama. Kana, yadda ake tafiyar da cinikayya kai tsaye yadda ya kamata, ya shimfida wani tubali na gaggauta bunkasa bangaren. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China