Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sana'ar noma kayan lambu a gundumar Bailang dake Tibet ta taimaka wajen dakile fatara
2020-09-29 16:13:34        cri

Dabarun inganta sana'ar noma ta amfani da rumfunan shuka kayan lambu a gundumar Bailang na birnin Xigaze dake jihar Tibet ta kasar Sin, sun samar da babbar damar fitar da mazauna gundumar daga kangin talauci.

Ana dai iya ganin runfunan shuka kayan lambu a jere a kwarin dake kewaye da tsaunukan gundumar, rumfunan dake cike da kayan lambu kamar su gurji, da yalo, da barkono.

Domin tabbatar da wannan fasaha ta taimakawa aikin yaki da talauci yadda ya kamata, mahukuntan gundumar Bailang sun sha alwashin jawo masu zuba jari, da kuma noma kayan lambu masu karbuwa a yankin. Tuni kuma kamfanonin ayyukan noma daga lardin Shandong da birnin Shanghai suka kafa wuraren aiki a wannan yanki.

Tun kafa babbar cibiyar lura da ayyukan gona a wannan yanki, kawo yanzu, cibiyar ta biya mazauna wurin diyyar filayen noma da dama, wadanda darajar su ta kai kusan kudin Sin yuan miliyan 20, ta kuma raba ribar alfanun filayen da aka yi hayar su, kan kusan kudin Sin yuan miliyan 5, tare da daukar hanyar manoma da makiyaya kusan 200.

Bisa karbuwa daga kamfanonin sarrafa kayan gona dake wurin, sashen kayan lambu na Bailang ya samu matukar bunkasuwa. Ya zuwa yanzu, akwai iyalai mazauna wurin sama da 3,200 dake cin gajiya daga sana'ar noman kayan marmari, da kayan lambun da ake nomawa a wurin. A shekarar 2019 kadai, kiyasin kudaden da ko wanen iyalin wurin ke samu ya karu, da sama da kudin Sin yuan 10,000. (Saminu )

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China