Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafafen watsa labarai sun fara rijistar halartar bikin baje kolin CIIE karo na uku a ranar 24 ga wata
2020-10-02 19:12:47        cri

Rahotanni daga kasar Sin na cewa, za a bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da kuma fitarwa daga kasar Sin na kasa da kasa karo na uku(CIIE) a ranar 5 ga watan Nuwanban wannan shekara a birnin Shanghai. Kana a ranar 24 ga watan Satumba kuma, an bude dandalin da kafafen yada labarai da za su halarci bikin za su yi rijista, inda ake saran za a rufe wannan dandali a ranar 20 ga watan Oktoba.

A saboda matakan kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Bikin baje kolin na CIIE karo na uku, zai gayyaci 'yan jaridu na cikin gida da na ketare dake nan kasar Sin, da 'yan jaridu dake yankunan musamman na Hong Kong da Macao da Taiwan. Za kuma su yi rijista ta shafuka da manhajan Wechat da aka tanada a hukumance. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China