Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kayayyakin gargajiya da wani dan jihar Xinjiang ya adana sun shaida ci gaban da aka samu wajen kawar da talauci a wurin
2020-09-18 11:04:54        cri

Ugabula Ahemati yana zaune a garin Wutamu dake gundumar Ruoqiang na yankin Bayingol na Mongoliya mai cin gashin kansa a jihar Xinjiang, wurin da ke kewaye da hamada. Tsakar gidansa ba shi da bambanci da na gidajen sauran mutane ba, sai dai idan an shiga dakinsa, za a yi mamaki.

Ugabula Ahemati mai shekaru 59 da haifuwa, ya taba aiki a garin a fannin harkokin al'adu, ya tattara kayayyakin gargajiya da dama bisa sha'awarsa. Daga baya, ya kashe kudin Sin RMB Yuan fiye da dubu 200, don gina wani dakin adana kayayyakin gargajiya na jama'a a cikin dakinsa.

Ban da wadannan kayayyakin gargajiya, ya adana wasu zane-zane da ya yi, wadanda suka bayyana salonsa, da ma al'adun wurin, abubuwan da ya kyautata ingancin dakinsa na adana kayayyakin gargajiya.

Tun daga shekarar 2001, Ugabula Ahemati ya kan yi zane da jan dabino. A cikin zanensa ya bayyana yadda ake shuka dabino, da sarrafa su har ma da sayar da su. Yanzu gundumar Ruoqiang ta zama shahararren garin jan dabino a kasar Sin, wanda hakan ya zama matakin samar da wadata ga wurin, inda kudin shigar ko wane manomi, da makiyayi na wurin a ko wace shekara, ya kai RMB Yuan dubu 33 a shekarar 2019, daga dubu 2.2 a shekarar 2001. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China