Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Furanni na taimakawa gundumar Dounan fita daga kangin talauci
2020-09-17 16:25:15        cri

Kasuwar sayar da furanni ta Dounan na birnin Kunming na lardin Yunnan, kasuwa ce irin wannan mafi girma a nahiyar Asiya. Gundumar Dounan ta fidda wata hanyar zaman wadata ta dogaro da furani. Yanzu, mazaunan wuri na jin dadin zaman rayuwa.

Karshen shekaru 80 na karni na 20, manoma sun fara gwada shuka furanni cikin gonaki, gwamnatin wurin ta kafa kasuwa don taimaka musu wajen sayar da furanni. Kasuwa ta rika samun bunkasuwa, manoma kuma sun dogaro da wannan sha'ani sun samu arziki.

Amma, cutar COVID-19 da ta bullo ba zato ba tsamani ta illata wannan sha'ani a Dounan. Saboda ganin haka, gwamnatin wuri ta ba da taimako wajen kafa wani dandali ta hanyar watsa shiri kai tsaye, da sayar da furanni a kan Intanet don habaka kasuwa.

A cikin farkon watanni 7 na bana da suka gabata, yawan kudin dake shafar wannan sha'ani ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 3.52, wanda ya kai matsayi na makamancin lokaci na bara. Ya zuwa yanzu, manoma na gundumar Dounan, kowanensu na ya iya samun kudin shiga kimanin RMB Yuan dubu 30 a kowace shekara, sha'anin kuma ya samar da guraben aikin yi ga mutane dake kewayen yankin kimanin dubu 130. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China