Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: kafofin fasahar sadarwa sun taimaka wajen raya ilimi a Afirka a gabar da ake tsaka da fama da COVID-19
2020-09-17 10:03:05        cri
Sakamakon wani binciken jin ra'ayin al'umma da aka fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, ya nuna cewa, nahiyar Afirka ta amfana matuka da hanyoyin fasahar sadarwa, wajen raya ilimi a lokacin da ake tsaka da yaki da cutar COVID-19.

Rahoton binciken da aka fitar a jiya Laraba, ya ce da yawa daga kasashen nahiyar, sun lura da muhimmancin koyon ilimi ta amfani da na'urorin zamani, a gabar da aka rufe kusan dukkanin makarantu, don dakile yaduwar cutar.

Rahoton mai taken "Tasirin COVID-19 kan ilimi a Afirka, da tasirin amfani da fasahar zamani," ya ce annobar ta tilastawa gwamnatoci daukar matakai na fifita gudanar da darussa ta na'urori, a kanana da manyan makarantu.

Manyan masu ruwa da tsaki a fannin ba da ilimi, da malamai daga kasashen Afirka 52 ne suka gudanar da aikin binciken. Sun kuma amince cewa, samar da manyan damammaki na amfani fasahar sadarwa, ya saukakawa dalibai wajen daukar darussa, a gabar da aka dage shiga ajujuwa don daukar darussa. Kaza lika rahoton ya zayyana wadatacciyar wutar lantarki, da na'urorin koyo, da jari a fannin, tare da layukan intanet masu sauri, a matsayin ginshikan wanzar da koyo da koyarwa a Afirka, lokacin da aka rufe makarantu sakamakon bullar COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China