Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar Afrika ta ce inganta tsarin mallakar gonaki jigo ne na samar da abinci ga nahiyar
2020-09-15 11:08:19        cri

Wata kungiyar Afrika ta ce damar da kasashen Afrika ke da shi wajen ciyar da kasashensu a daidai lokacin da duniya ke fuskantar matsalolin sauyin yanayi gami da annobar COVID-19, ya dogara ne kan yadda aka inganta tsarin kula da mallakar gonakin noma a shiyyar.

Audace Kubwimana, jami'in shirin gamayyar kula da filaye na kasa da kasa a Afrika, wato ILC Africa, a takaice, ya ce bunkasa tsarin kula da filaye a nahiyar wani muhimmin jigo ne wajen kawar da yunwa da kuma tinkarar matsalolin sauyin yanayi.

Ya ce matsalar kwararar farin dango, da tada rikice-rikice, da amfani da tsoffin manufofi, gami da matsalolin sauyin yanayi, sun yi matukar haifar da koma baya wajen yin sauye sauye a tsarin mallakar gonaki a Afrika. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China