Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sin ta ware kudi yuan biliyan 70 don raya ayyukan malamai a kauyuka
2020-09-14 13:22:46        cri

Ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta ba da labarin cewa, a lokacin gudanar da shirin shekaru biyar biyar karo na 13 game da ci gaban tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma, gwamnatin kasar ta samar da RMB yuan biliyan 70, don nuna goyon baya da ba da jagoranci ga kananan hukumomi wajen karfafa ayyukan malamai a karkara, da kuma kara ingancin aikin ba da ilimi.

A yayin shirin shekaru biyar biyar karo na 14 kuma, gwamnatin kasar za ta ci gaba da kyautata manufofi da makatan da batun ya shafa, da kyautata tsarin samar da kudin, da nufin goyon baya, da jagorantar kananan hukumomi wajen dora muhimmanci kan inganta ayyukan malamai, da kara ingancin aikin malamai a karkara. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China