Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin firaministan Sin ya jaddada muhimmancin inganta girbin amfanin gona a lokacin kaka
2020-09-14 10:31:54        cri

Mataimakin firaministan kasar Sin Hu Chunhua ya jaddada muhimmancin kyautata ayyukan gona domin samun yalwar amfanin gona a lokacin kakar girbe amfanin gonar.

Da yake tsokaci ya nuna cewa, ana samun sama da kashi 70 bisa 100 na nau'in hatsin kasar a kowace shekara a lokacin kakar girbin amfanin gona, Hu ya bukaci hukumomin yankuna da su dauki kwararan matakai domin tabbatar da ganin an samu yalwar amfanin gona a lokacin kakar girbi, ya bayyana hakan ne a lokacin rangadin da ya kai a yankin Heilongjiang, lardin mafi girma da ya fi samar da hatsi a kasar.

Ya ce, ya kamata hukumomin kananan yankunan kasar su gudanar da ayyuka bisa tsarin kiyaye dokoki domin farfado da ayyukan gona bayan fuskantar bala'u, da nufin rage tasirin annobar iska, da fari, da ambaliyar ruwa, wadanda suka shafi aikin samar da hatsi.

Hu, ya bukaci a yi cikakken shiri a lokacin kakar girbi, a karfafa sanya ido kan hasashen yanayin ruwan sama, da bunkasa shirin adana amfanin gona yadda ya kamata. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China