Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 50 sun mutu a DRC a ruftawar ramin hakar ma'adanai
2020-09-13 16:08:50        cri

A kalla mutane 50 ne suka mutu bayan da wani ramin hakar ma'adanin zinare ya rufta a gabashin jamhuriyar demokaradiyyar Kongo, DRC, hukumomin kasar sun sanar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

Hadarin ya faru ne a ranar Juma'a a garin Kamituga dake kudancin lardin Kivu, bayan wani mamakon ruwan sama da aka shafe kwanaki ana shekawa, lamarin da ta haifar da zaftarewar kasa, inda har yanzu ake ci gaba da gudanar da bincike.

Gwamnan lardin Theo Ngwabidje Kasi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar ranar Asabar, inda ya bayyana cewa, mafi yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su matasa ne, har ma da kananan yara. Masu aikin ceto suna ci gaba da zakulo gawarwaki tare da samar da tallafi.

Kafafen yada labaran cikin gidan kasar sun rawaito wani da ya tsira da ransa ya bayyana cewa, sama da mutane 50 ne suke cikin ramin wanda ruwa ya malala cikinsa.

Magajin garin Kamituga, Alexandre Bundya, ya ayyana makokin kwanaki biyu, kana ya bukaci mazauna yankin su taimakawa ma'aikatan ceto domin zakulo gawarwakin dake karkashin kasa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China