Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An amince da kafa gwamnatin rikon kwarya ta watanni 18 a Mali
2020-09-13 16:03:37        cri

Sojojin dake riki da madafun ikon kasar Mali sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya ta tsawon watanni 18, kuma za a nada shugaban kasar na rikon kwaryar da mataimakinsa daga cikin kwamitin dakarun sojojin kasar wato CNSP, Moussa Camara, babban jami'i mai shiga tsakani wanda ya tattauna da dukkan bangarorin siyasar kasar shi ne ya bayyana hakan a ranar Asabar.

A bisa ga tsarin yarjejeniyar kafa gwamnatin rikon kwaryar, wanda mahalarta kimanin 500 daga bangarori daban daban na kasar suka amince da shi bayan tuntuba ta tsawon kwanaki uku, an bayyana cewa, wanda za a nada shugaban kasar zai iya kasancewa soja ko kuma farar hula.

Baya ga shugaban kasar na rikon kwarya da mataimaki ko mataimakiyarsa, za a kafa gwamnati ne mai kunshe da mambobi 25 mafi yawa, karkashin jagorancin firaminista wanda shugaban kasar na rikon kwarya zai nada bisa ga tsarin dokar kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi a halin yanzu.

A ranar 18 ga watan Agusta ne sojojin kasar Mali suka kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita, da firaministan kasar Boubou Cisse, inda suka garzaya da su zuwa sansanin sojojin Soundiata Keita dake kusa da Bamako, daga bisani shugaban ya ayyana yin murabus tare da sanar da rusa majalisar dokokin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China