Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan al-Shabab 3 sun mutu a kusa da kan iyakar Kenya da Somalia
2020-09-12 17:06:33        cri
Yan sandan kasar Kenya sun tabbatar da mutuwar mayakan 'yan ta'addan kungiyar al-Shabab uku kana hudu daga cikinsu sun samu raunuka a ranar Alhamis, a sakamakon wasu boma boman da suka jera a gefen titi inda suke kokarin kaddamar da hari a yankin Garissa kusa da kan iyakar kasar Somali.

Rono Bunei, kwamandan hukumar 'yan sandan shiyyar arewa maso gabashin yankin, ya ce, 'yan ta'addan sun mutu ne sakamakon abubuwan fashewar da suka tashi dasu a lokacin da suke kokarin jera su a yankin Fafi dake shiyyar arewa maso gabashin kasar Kenya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China