Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu ta bukaci allurar rigakafin COVID-19 su amfanar da Afrika
2020-09-11 14:50:16        cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya jaddada cewa ya kamata kasashen Afrika su amfana daga allurar rigakafin COVID-19 da ake kokarin samarwa.

Ramaphosa ya ce, kamata ya yi a sanya mutanen Afrika cikin wadanda za a yiwa gwajin rigakafin domin tabbatar da ganin rigakafin ya dace da yanayin mutanen Afrika, ya bayyana hakan ne a taron majalisar samar da rigakafin annobar COVID-19 wato ACT-A a takaice, wanda aka gudanar ta kafar bidiyo.

Ramaphosa ya ce, tsarin kiwon lafiyar duniya na bai daya ba zai cimma nasara ba idan har allurar rigakafin cutar COVID-19 an samar da su ne kadai ga kasashen da suke da arziki ta fuskar bincike, da masana'antu, da rarraba kayayyaki da ayyukan hidima.

Shugaba Ramaphosa ya bukaci dukkan kasashen duniya da su tallafawa shirin da ake gudanarwar na duniya a halin yanzu wajen samar da kudaden samar da rigakafin cutar COVID-19.

Ban da wannan kuma shugaban ya ce, kamar yadda wasu suka riga suka yi, akwai bukatar gwamnatoci su samar da tallafin samar da allurar rigakafin domin samun kwarin gwiwar samar da isassun rigakafin akan lokaci.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China