Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da ambaliyar ruwa ta halaka a Nijar ya karu zuwa 71
2020-09-11 10:51:48        cri
Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa, ambaliyar ruwa da ta shafi sassan kasar, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta shatatawa, ta yi sanadiyar rayukan mutane kusan 71 , baya ga gidaje kimanin33,000 da suka lalace.

Ministan ayyukan jin kai da daidaita bala'u na kasar Lawan Magagi, ya bayyana cewa, gwamnati tana daukar matakan da suka dace, don sake tsugunar da wadanda bala'in ya shafa. A don haka tana bukaci bangarorin daban-daban na al'umma dake kasar, da su taimaka.

Galibi dai, lokacin damina a kasar ta Nijar, yana farawa ne, daga watan Yuli zuwa Satumban kowa ce shekara. A shekarar 2012 ma, kasar ta yi fama da matsalar ambaliyar ruwa, da ba a taba ganin irinta ba cikin shekaru 80, inda har mutane 88 suka sheka barzahu, baya ga masifu sama da dubu 500.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China