Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da takardar bayani game da matsayinta dangane da cikar MDD shekaru 75 da kafuwa
2020-09-10 20:57:31        cri
A yau Alhamis 10 ga watan Satumba ne, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta fitar da takardar bayani game da matsayar kasar Sin, dangane da cikar MDD shekaru 75 da kafuwa. Takardar ta yi fashin baki game da mahangar kasar game da tasirin MDDr, da yanayin da ake ciki a harkoki na kasa da kasa, da batun ci gaba mai dorewa, da hadin gwiwa a fannin yaki da annobar Covid-19.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian ne ya gabatar da wannan takardar bayani, gaban mahalarta taron ganawa da 'yan jaridu da aka shirya.

Yayin da yake gabatarwar, Zhao ya ce "Takardar ta yi nuni da yadda ya kamata sassan kasa da kasa, su yi amfani da zagayowar wannan rana, a matsayin muhimmin lokaci na ingiza hadin gwiwa, wajen kare nasarar da aka cimma a fannin yaki da 'yan mulkin danniya, su kuma kaucewa daukar matakai na kashin kai, da watsi da tunanin mulkin mulaka'u da siyasar fin karfi. Kaza lika ya dace kasashen duniya su goyi bayan cudanyar sassa daban daban, su kare dalilan kafuwa, da ka'idojin MDD, su martaba tsarin gudanarwa na duniya karkashin laimar MDD. Ya ce Sin a shirye take, ta yi aiki tare da sauran sassan kasa da kasa, wajen gina al'umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China