Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Malamai na gari, ya kamata ya kiyaye wadannan…
2020-09-10 13:26:25        cri

 

Yau Alhamis rana ce ta musamman da gwamnatin kasar Sin ta kebe domin nuna girmamawa ga masu aikin malanta. Al'ummar kasar Sin suna da al'adar girmama malamai, wannan ne ya sa aka kebe wannan rana don kara daukaka matsayin malamai.

Sa'an nan a nasa bangare, shugaba Xi Jinping na kasar, ya taba bayyana wasu abubuwan da ya kamata a yi, idan har ana son zama malamai masu nagarta.

Ya ce, ya kamata, malami na gari ya zama mai kishin kasa da al'umma. Sa'an nan ya yi kokarin zama abin koyi a fannin dabi'a da halayyar kirki. Ban da wannan kuma, dole ne a matsayin malami na gari, ya kasance mai nuna daidaito yayin da yake koyar da dalibai daban daban. Haka kuma ya kasance mai hakuri, yayin koyar da su abubuwan da ba su iya ba, sa'an nan ya yi kokarin neman ganin fannonin da suke da hazaka, don nuna ma daliban hanyoyin da za su bi don zama kwararru, wadanda za su iya samar da gudunmawa ga kasa da ma al'umma baki daya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China