Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta sake inganta sassan masana'antunta don kara janyo masu sha'awar zuba jari na ketare
2020-09-09 10:23:52        cri
Mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Wang Shouwen, ya bayyana cewa, kasarsa za ta kara sanya wasu abubuwa a jerin ayyukan masana'antunta, don kara janyo masu sha'awar zuba jari na ketare da taimakawa kamfanoni masu jarin waje, kara cin gajiyar manufofi na gatanci da kasar ta bullo da su.

Wang wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a bikin baje kolin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa ta kafar bidiyo, ya ce ma'aikatarsa za ta ci gaba da rage sassa da a baya aka haramtawa baki zuba jari a ciki, da fafada harkokin na kasuwanci don kara janyo masu zuba jari na ketare, da kara cin gajiyar babbar kasuwa da damammaki dake kasar Sin tare da baki masu zuba jari na ketare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China