Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan tana hasashen ruwan kogin Nilu zai ragu bayan ambaliya
2020-09-09 10:18:30        cri

Ministan noman rani da albarkatun ruwa na kasar Sudan Yasir Abbas, ya bayyana cewa, akwai yiwuwar ruwan dake kogin Nilu zai fara raguwa sannu a hankali tun daga jiya Talata.

Yasir ya bayyana cewa, yadda ruwan sama kamar da bakin kwarya ke kwarara tsaunin Habasha, na daga cikin manyan dalilan dake haddasa tarihi na ambaliyar kogin na Nilu.

Sai dai kuma, ministan ya karyata cewa, babbar madatsar ruwan nan da Habashe ke son ginawa(GERD) ita ce ta haddasa ambaliyar ruwan a kasar ta Sudan, kuma matsalar ambaliyar ba za ta faru a Sudan bayan an kammala aikin babban madatsar ruwan ba, wadda ita ce za ta daidaita gudun ruwan kogin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China