Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana taimakawa nakasassu wajen kyautata zaman rayuwarsu a birnin Tangshan na lardin Hebei
2020-09-08 15:53:43        cri

Bayan babbar girgizar kasa da ta abku a birnin Tangshan dake lardin Hebei na kasar Sin, an shiga taimakawa nakasassu dake wurin a fannoni daban daban. An kara kula da mazaunen birnin, da kara karfafa musu imani da kwarin gwiwa ta hanyar inganta rayuwarsu a zamanin yanzu.

"Mutane masu lafiya gami da nakasassu duk suna yin rayuwa mai kyau." A cewar shugaban kasar Sin Xi Jinping, wannan ya taimakawa Wang Dan mai shekaru 38 kokarin kyautata rayuwarta. A sakamakon wata cuta da ta ganuwa da ita, Wang Dan ta gamu da nakasa. Bisa goyon bayan da gwamnatin birnin Tangshan da hukumar kula da nakasassu ta birnin suka nuna mata, ta kafa wani kamfanin saka kayayyakin hannu na gargajiya. Kana gwamnatin ta samar mata wurin da za ta rika wannan aikin ba tare da biyan kudi ba, kuma hukumar kula da nakasassu ta birnin ta ba ta Yuan dubu 50 don bude kamfanin. A sa'i daya kuma, kamfanin Wang Dan ya taimakawa nakasassu fiye da 100 don su kara samun kudin shiga ta hanyar yin aikin a kamfanin.

Babu wani nakasashe ko daya da aka bari, a kokarin da ake na raya zaman al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni. Tun daga shekarar 2017 zuwa 2019, yawan jarin da birnin ya zuba a wannan fanni ya kai Yuan miliyan 310, wanda ya amfanawa nakasassu dubu 700. Bisa kokari da kulawar da gwamnatin birnin ta nuna musu, nakasassu suna kokarin kyautata rayuwarsu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China