Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kaddamar da shirin tsaron bayanai na duniya
2020-09-08 10:45:38        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana a yayin taron karawa juna sani da aka shirya yau game da yadda duniya take tafiyar da harkokin fasahar zamani cewa, kasar Sin za ta shiga a dama da ita a tattaunawar tsaron muhimman bayanai yayin taron MDD, da G20, da na BRICS da sauran dandalin kasa da kasa. Haka kuma, a shirye kasar Sin ta ke, ta bayar da gudumawar ruhin Sinawa, na karfafa yadda ake tafiyar da harkokin fasahar sadarwa a duniya.

Bugu da kari, a shirye kasar Sin ta ke, ta kaddamar da shirin tsaron bayanai na duniya, tana kuma maraba da duk kan bangarorin dake da sha'awar shiga a dama da su, duk a kokarin ganin an magance sabbin matsaloli da kalubaloli daka iya bijirowa a wannan fanni.

Wang ya yi nuni da cewa, ya kamata a dauki matakan da suka dace, don magance hadari da kalubalolin tsaron bayanai, musamman manufofi uku na hadin gwiwar bangarori daban-daban, da bunkasa tsaro. Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin, za ta martaba ka'idojin tsaron bayanai, kuma ba ta taba neman kamfanonin kasarta, su baiwa gwamnatin kasar Sin bayanan ketare ba, don keta dokokin sauran kasashe. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China