Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WFP: Ana hasashen mutane miliyan 100 za su fada kangin talauci sakamakon COVID-19
2020-09-07 10:13:15        cri

Wakilin shirin samar da abinci na MDD dake kasar Sin Maha Ahmed, ya bayyana cewa, kimanin mutane miliyan 70 zuwa miliyan 100 ne, ake zaton za su fada kangin talauci a wannan shekara a fadin duniya, sakamakon cutar numfashi ta COVID-19. A don haka, shirin na WFP ke neman taimakon kudade, don samar da abinci ga mutane sama da miliyan 100 dake matukar bukata.

Da yake karin haske yayin da yake jawabi a taron zuba jari kan aikin gyara kayayyakin amfanin gona karo na 23 da aka bude jiya a birnin Zhumadian dake lardin Henan na kasar Sin, Maha Ahmed, ya ce shirin WPF, ya yi kiyasin cewa, adadin mutanen dake fuskantar karancin abinci a kasashe 79 da shirin ke da ofisoshi, na iya karuwa da kaso 80 cikin 100, daga mutane miliyan 149 kafin barkewar annobar zuwa mutane miliyan 270 ya zuwa karshen shekarar 2020, sannan duk wani mai karamin karfi ko mai matsakaicin kudin shiga na iya fuskantar barazana.

A don haka, jami'in ya ce, shirin ya tashi haikan wajen neman tallafin kudade, don taimakawa rukunonin mutane masu rauni, ta hanyar ba su kudin tallafi, da inganta hidimomin samar da abinci mai gina jiki da tsare-tsaren samar da taimakon abinci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China