Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ciniki mai amfani da fasahar sadarwa zai ingiza bude kofar Sin ga ketare
2020-09-06 16:12:55        cri
Jiya Asabar, an gudanar da bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020. A wannan rana kuma, an kira taron koli na bunkasuwar cinikin ta hanyar amfani da fasahar sadarwa a cibiyar taron kasar Sin, wanda ya kasance daya daga cikin wasu manyan dandalolin tattaunawa na bikin. Ministan masan'anatu da sadarwa na kasar Xiao Yaqing ya gabatar da ci gaban da Sin take samu a wannan fanni, yana mai cewa, Sin tana samun bunkasuwa mai armashi a wannan fanni, a cikin shekarar 2019 da ta shude, yawan kudin dake shafar wannan fanni ya kai kudin Sin RMB triliyan 35.8, wanda ya kai kashi 36.2% na dukkan GDP, matakin da ya zama wani babban tushe dake goyon bayan bunkasuwar tattalin arzikin Sin mai inganci.

Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Wang Bingnan, ya bayyana cewa, bisa kididdigar da Sin ta bayar, cinikayyar shigi da fice dake da alaka da fasahar sadarwa a shekarar 2019, ya kai dala biliyan 203.6, wanda ya kai kashi 26% na dukannin cinikayyar bada hidima, wanda ya karu da kashi 6.7% bisa na makamancin lokaci na shekarar 2018.

Masu halartar biki da ma masana sun bayyana cewa, irin wannan ciniki zai kara taka rawa wajen zamanintar da sauran masan'antu na gargajiya don su samu kyautatuwa, a hannu guda kuma, fasahar sadarwa zata yi kwaskwarima a fannin kirkire-kirkire da ingiza sabbin nau'o'in ciniki, matakin da zai daga matsayin kasar Sin ta fuskar karfin takara a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China