Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu sabbin mutane wadanda suka harbu da cutar COVID-19 a cikin gidan kasar Sin
2020-09-05 17:44:44        cri
A jiya Juma'a, babu sabbin mutane wadanda suka harbu da cutar COVID-19 a cikin gidan babban yankin kasar Sin, inji hukumar lafiyar kasar wacce ta sanar a yau Asabar.

An samu wasu mutane 10 da suka shigo da cutar daga kasashen ketare a ranar Juma'a, kamar yadda hukumar ta tabbatar da hakan. Kana babu rahoton ko da mutum guda da ya mutu sakamakon cutar a kasar Sin a ranar Juma'a, kamar yadda hukumar ta bayyana.

A cewar hukumar an sallami wasu majinyata 21 daga asibitoci da suka kamu da COVID-19 bayan sun warke daga cutar, a babban yankin kasar ta Sin, a jiya Juma'a. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China