Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su kara goyon bayan WHO
2020-09-04 20:20:11        cri

Yau Jumma'a madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a nan Beijing cewa, kasar Sin tana kira ga kasashen duniya da su kara goyon bayan WHO da kuma biyan kudaden su a karo-karo a matsayinsu na mambar hukumar.

An ruwaito cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta sanar a ranar 3 ga wata cewa, za ta biya MDD kudin da ya rage ta biya hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO a matsayin mambar hukumar a shekarar 2020, sa'an nan Amurka za ta rage tuntubar WHO sannu a hankali

Dangane da lamarin, madam Hua Chunying ta ce, yayin da ake fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, duk wanda yake cin zalin WHO, har ma ya yi mata sharri, bai damu da rayukan mutane ba, kana ya yi illata akidar jin kai, da kuma kawo cikas ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar. Kuma dukkan kasashen duniya na adawa da shi. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China