Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gina laburare mafi tsayi na Sin a birnin Tianjin
2020-09-04 15:37:08        cri

A 'yan shekarun nan, birnin Tianjin ya dukufa wajen raya harkokin al'adu na birnin. Yanzu, an gina wani laburare na zamani cikin babbar hasumiyar talebijin na birnin Tianjin, wanda ya zama wuri mai farin jini da jama'ar birnin Tianjin suke son zuwa.

Hasumiyar talebijin ta birnin Tianjin ta zama babbar alama ta birnin, a ranar 18 ga watan Janairun bana, an bude laburaren mafi tsayi na kasar Sin cikin wannan hasumiya, wato laburaren Tianta Xi'an.

Yankin yawon shakatawa na tabkin Tianta da hukumar al'adu da yawon shakatawa ta yankin Hexi na birnin Tianjin suka yi hadin gwiwar gina wannan laburare, wanda fadinsa ya kai muraba'in mita 660, cikinsa akwai litattafai 8500. Kana, mataimakin shugaban hukumar raya al'adu da yawon shakatawa ta Hexi Qu Weihe, ya bayyana cewa, a halin yanzu an kafa laburare na hallayar musamman guda 10 a birnin Tianjin, domin sa kaimi ga al'ummomin birnin don su kara karatu.

Mataimakin babban manajan kamfanin raya al'adu da yawon shakatawa na tabkin Tianta Wang Yan ya ce, wurin karanta litattafai wuri ne mai muhimmanci wajen karfafa wayewar kai, zai ba da gudummawa matuka wajen kare al'adun gargajiya, da ba da ilmi. Kuma ya nuna fatan cewa, dukkanin al'ummomin birnin Tianjin za su ga canje-canje a birnin Tianjin, da bude idonsu, da kara ilminsu, da kuma jin dadin zaman rayuwarsu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China